Saturday, November 2, 2019

MAULIDIN ANNABI YAFI QARFIN HUJJA

MAULUDiN ANNABI S.A.W YAFI QARFIN HUJJA.
.
Watarana an tambayi SHEIKH IBRAHIM INYASS
menene hujjan yin MAULUD ?
.
Sai Shehu yace rashin Hujja Maulidi shine ya kawo hujjan mu na yin mauludin
.
Domin akwai Abunda yafi Qarfin hujja
Shehu yace baka ga duk Qur'ani, ba inda Allah
yacema UWA ta so DAN ta ba?
.
Ai Allah bai cema UWA ta so DAN taba, saboda bata bukata sai ance mata ta so shi zata so shi. Domin Allah ya riga ya shuka son DAN acikin UWAN,
.
Amma shi DAN da a kasan zai iya Qin biyayya baka ga wuri daban daban Allah yake umartarsa da bin iyaye ba?

Watarana an taba haduwa da wata mata aka
nunamata wani malami "imamul Faharrazi" aka ce mata kinga malamin can zai iya baki Hujja dubu akan samuwan Allah
.
Sai matan tace "Allah sarki miskini!
Ai yana da shakka dubu ne a zuciyarshi shi yasa har zai iya samo hujja dubu in ba haka ba ya za'ayi mutum, in ba mahaukaci ba ya É—auko "touch light" da rana kuma yace wai yana neman Rana?
.
Duk girman hujja ai bata kai "touch light" rana tare da ubangiji ba, Allah da ya kira kansa "Azzahiru" kuma yake bukatan wata hujja tazo ta bayyana dashi?

Ai Lamarin Akwai Abun dubawa

S.A.WMAULIDIN ANNABI YAFI QARFIN JUJJAH

No comments:

Post a Comment